Al’ummar
Hausawa sun daɗe suna hulɗa da iskoki. Tarihi
ya nuna wannan hulɗa ta samo asali ne tun lokacin da suke cikin addininsu na
gargajiya. Bincike a kan addinin Bahaushe na gargajiya ya samu karɓuwa sosai ga masana al’adun Hausawa. A yau, goshin ƙarni na ashirin da ɗaya Hausawa sun buɗe wani sabon shafi na hulɗa da iskoki. A da, ’yan bori da bokaye da malaman tsibbu su ke cin
karensu ba babbaka a kan sha’anin hulɗa da iskoki.
Yanzu an sami rukunin wasu malaman addini da suke hulɗa da iskoki ta hanyar ruƙiyya[1], domin warkar da cututtukan da…
Yakubu Aliyu
Gobir
Department of
Nigerian Languages
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto
È08035605024,
email: yagobir@yahoo.co.uk
1.0
Gabatarwa
Al’ummar Hausawa sun daɗe suna hulɗa da iskoki. Tarihi ya nuna wannan hulɗa ta samo asali ne tun lokacin da suke cikin addininsu na
gargajiya. Bincike a kan addinin Bahaushe na gargajiya ya samu karɓuwa sosai ga masana al’adun Hausawa. A yau, goshin ƙarni na ashirin da ɗaya Hausawa sun buɗe wani sabon shafi na hulɗa da iskoki. A da, ’yan bori da bokaye da malaman
tsibbu su ke cin karensu ba babbaka a kan sha’anin hulɗa da iskoki. Yanzu an sami rukunin wasu malaman
addini da suke hulɗa da iskoki ta hanyar ruƙiyya[2], domin warkar da cututtukan da suka shafi iskoki. Daga cikin waɗannan cututtukan da suka shafi iskoki akwai abin
da Hausawa ke kira, ‘Namijin Dare’ ko ‘Macen Dare’, wato hulɗar soyayya da ke gudana tsakanin ɗan Adam da iskoki (Tsakanin mace mutum da aljani namji ko
tsakanin aljana da mutum namiji). Gano yadda Hausawa ke warkar da wannan cuta
shi ne maƙasudin wannan maƙala.
2.0 Waiwaye
Hausawa
na cewa ‘waiwaye adon tafiya.’ Bisa ga haka, akwai bukatar waiwaye don mu ji
matsayin iskoki a idon Bahaushe. Masana al’adun Hausawa irin su Greenberg,
J. (1946), Besmer, F.E. (1973), Ibrahim S.M. (1982), Bunza, A.M. (1990), Ismaila,
H.A (1991), Iliyasu, G. (2000) da sauransu Greenberg,
J. (1946), Besmer, F.E. (1973), Ibrahim S.M. (1982), Bunza, A.M. (1990), Ismaila,
H.A (1991), Iliyasu, G. (2000) da sauransu, sun yi
rubuce-rubuce da dama a kan iskoki da matsayinsu a rayuwar Bahaushe. Sun tabbatar da imanin Bahaushe a kan samuwar iskoki,
duk da yake ba ya ganin su amma ya yi imani da samuwar su da kuma kasancewar su
buwayayyi, masu ban tsoro, masu ƙarfi a kan
mutane kuma masu iya cuta musu. Za a iya fahintar haka tun daga sunayen da
Bahaushe ke kiran su da shi. Ya kira su ‘iskoki’ ne domin ba ya ganin su
kamar yadda ba ya ganin iskan da muke shaƙa. Yana kiran su ‘masu abu’ don suna nuna isa ga duk abin
da suke nufi aikatawa ko suke bukata. Yana kiran su ‘mutantani’ saboda sun yi tarayya da mutane ta ɓangaren jinsi da hali. Wato suna da jinsin maza da mata,
suna aure da haihuwa da cin abinci da sauransu.[3] Kodayake imanin Bahaushe a da, ya yarda cewa, iskoki
ba su mutuwa, amma yanzu malaman rukiyya, (Iliyasu: 2000) sun tabbatar da cewa iskoki
suna mutuwa. Sai dai suna da tsawon rayuwa ba kamar ta mutane ba. Ta fuskar
yadda Bahaushe ya fahinci iskoki kuwa, ’yan bori na ganin cewa akwai
farare da baƙaƙe. Fararen su ne masu sauƙin kai da daɗin hulɗa, saɓanin waɗanda ake kira baƙaƙe masu mugunta da sharri. Haka su ma masu ruƙiyya, sun kasa iskoki gida biyu dangane da
mu’amala da su. Waɗanda ’yan bori ke kira farare, su masu ruƙiyya ke kira Musulmi, Kafirai kuwa su ne baƙaƙe.
Bayan bayyanar Musulunci a ƙasar Hausa, Bahaushe ya fara amfani da sunaye irin su
‘Aljani’ da Ira’izzai, da Rafani da Shaiɗan, da sauransu. Dalili kuwa saboda waɗannan sunaye sun zo a cikin nassin Alƙur’ani da Hadisin Manzon Allah (SAW). Saboda haka a yau,
Bahaushe ya fi amfani da waɗannan sunayen, saboda sun fi kusanci da addininsa na Musulunci.
3.0 Wuraren Zaman Iskoki
Kamar
yadda kowane abu mai rai ko maras rai yake da muhalli ko wurin zama, haka su ma
iskoki suke da nasu muhalli. Bahaushe ya yi imani cewa iskokin ƙasar Hausa ana samun su a ko’ina a ƙasar Hausa. Duk da haka, akan same su a wurare ayyanannu
kamar kan duwatsu ko gindin manyan itatuwa kamar su itacen kuka da tsamiya da
gawo da gamji da sauransu. Akan kuma same su a dokar daji ko a cikin ruwa da
gidajen tururuwa da faƙo da suri (ƙunƙuwa) da
sauransu. A cikin gari kuwa, ana samun su a mararrabar hanya da kangon gida da
maƙabarta da juji (wurin zuba shara) da sauransu. A cikin
gida kuwa ana samun su a ban-ɗaki da tsakar gida da ƙofar ɗaki da turakun dawaki da sauransu. A jikin mutane kuwa
suna zama a ko’ina cikin jiki, amma sun fi zama a cikin ƙwaƙwalwa.
Wannan yana da nasaba da kiran su ‘ƙwanƙwammai.’ Duk waɗannan wuraren da Hausawa ke riya cewa mazaunin iskoki
ne, mafi yawansu malaman ruƙiyya da
Musulunci sun tabbatar da haka.[4] Wannan tabbatarwar na daga cikin abubuwan da suka ƙara ƙaimin
imanin Bahaushe da iskoki, kuma ya ƙarfafa ci gaba da hulɗa da su, duk da samun wayewar kai na zamani da bunƙasar ilimin addini Musulunci.
4.0 Dalilan Hulɗa Tsakanin Iskoki da Mutane
Bayanan da suka gabata, za su iya gamsar da mu cewa lalle
akwai hulɗa tsakanin
iskoki da Hausawa. Masana al’adun Hausawa sun fitar da dalilai uku da ke
sa iskoki hulɗa da mutune. Dalilan kuwa su ne; ƙiyayya da
tsoro da kuma ƙauna[5]. Idan mutum ya cuta wa iskoki ta hanyar aibata wa
'ya'yansu ko tsofafinsu ko ƙona
gidansu ko kwarara wa gidansu ruwan zafi, da sauransu, to iskokin kan ƙulla ƙiyayya da
wannan mutum, su ɗauke shi
abokin gabar su, kuma su ɗauki niyyar ramuwa gare shi. Wannan zai kai ga iskokin su shige shi,
su raunana masa lafiyar jiki.
Haka kuma a dalilin tsoro mai tsanani, irin wanda ke
mantar da mutum tuna Allah, to lokacin iskoki na samun sauƙin shiga jikinsa, musamman idan mutum ba ya yi wa Allah ɗa’a. Haƙiƙa rashin yi wa Allah ɗa'a yana ƙara sa
mutum jin tsoro mai firgitarwa, kuma yana sa shaiɗan ya ƙara masa
jin tsoronsa, sai tsoron ya yi tasiri a kansa, kamar faɗar Allah (S.WT):
“Wancan,
shaiɗan ne kawai yake tsoratar da masoyansa.
To, kada ku ji tsoronsa, ku ji tsorona, idan
kun kasance
masu imani.” (Alkur'ani
sura 3: aya 175)
(Fassarar Shaikh Mahmud Gummi)
Sai
dalili na uku, wanda kuma shi ne
bagiren wannan takarda, wato dalilin ƙauna
ko soyayya. Idan iskoki
na sha’awar surar jikin mutum ko ɗabi’unsa da sauransu sai su nemi yin hulɗa da shi. A wajen irin wannan hulɗar, iskan kan bayyana cikin kamannun mutane
kyawawa ta yadda ba su tsoratar da abokin hulɗarsu. Wani lokaci sukan bayyana cikin surar mutumin da
aka sani. Hulɗar ƙauna ta kasu kashi biyu: Akwai hulɗa tsakanin jinsi ɗaya, wato kamar a samu hulɗa tsakanin namijin iska da namijin ɗan Adam, ko hulɗa tsakanin macen iska da macen ’yar Adam. Akwai
kuma hulɗar ƙauna ta bambancin jinsi. Wato tsakanin namijin iska
da macen ’yar Adam ko macen iska da namijin ɗan Adam. Daga cikin irin wannan hulɗa ake samun namijin
dare ko macen dare.
5.0 Ma’anar Namijin Dare/Macen Dare
Namijin
dare
ko Macen dare wani nau’in iska ne daga cikin iskoki wanda ke auren mace ‘yar Adam
yana saduwa da ita (jima’i), ko kuma iska mace ta auri mutum ɗan Adam ta rinƙa
saduwa da shi ta hanyar mafarki ko a farke, musamman cikin dare. Irin wannan
saduwa tana haddasa cututtuka ga jiki ko zuciyar ɗan Adam.
Malaman ruƙiyya na
kiran irin wannan iska da sunan ‘Aljanin/Aljanar soyayya’.
6.0
Aure Tsakanin Aljani da Mutum
Malaman addinin Musulunci, musamman waɗanda suka zurfafa a cikin sha’anin ruƙiyya da aikin asibiti, sun tofa albarkacin bakinsu
dangane da wannan matsala ta aure tsakanin aljani da ɗan Adam.[6] Abin da ya tabbata ga malaman ruƙiyya shi ne auren yana yiyuwa, amma bai halatta ba a
shari’a. Wato Namijin iska na iya saduwa da mace ’yar Adam, ko ɗan Adam ya sadu da macen iska, kuma su samu jin daɗi irin wanda ake ji na saduwa (jima’i), amma shari’a ta
yi ƙyama ga aikata haka. Saboda an tambayi Imam Malik ɗan Anas cewa wani aljani ya zo yana neman a ba shi wata
bazawara aure? Sai Imam Malik ya ce, “Ban ga illa ba ga haka, sai dai ina ƙyamar idan macen ta yi ciki aka tambaye ta, waye mijinki?
Ta ce ‘wani aljani’. To wannan zai haifar da ɓarna da fasadi a cikin Musulunci.”[7]
7.0 Dalilan
Shigar Namijin Dare/Macen Dare
Daga cikin dalilan da kan jawo shigar Namijin dare
ga mace su ne:
·
Tsiraitar da al'aura ga mace ko namiji cikin gida, kamar mace ta tsiraita
zindir ko ta sanya tufafi maras kauri, kuma ta zo ta tsaya gaban madubi, tana
mamakin kyawon kanta, idan aka yi rashin sa’a aljanin soyayya yana kusa, sai ya
yi sha’awar ta, kuma son ta ya kama shi sai ya shige ta[8].
·
Idan mace ko namiji suna kwantawa a tsiraice a waje, misali lokacin bazara,
kuma ba su ambaci sunan Allah ba, Namijin dare ko macen dare kan
yi sha’awarsu, kuma su shige su.
·
Idan mace ko namiji na shiga ban-ɗaki wajen wanka a tsiraice, ko shiga ruwa (gulbi ko
kududdufi) wajen wanka a tsiraice kuma ba a ambaci sunan Allah ba. Namijin
dare ko macen dare kan samu sauƙin shigarsu kuma ya aure ta ko ta aure shi.
·
Idan mace na bayyanar da ƙawarta a
titi ko bainar jama’a, Namijin dare na iya kai mata hari.
·
Idan mutum na saduwa da iyali ba tare da ambaton sunan Allah ba, shaiɗanin aljani kan samu damar shiga jikinsa ko jikin iyalin.
·
Idan mutum ya sadu da iyalinsa alhali tana haila namijin dare zai
riga shi gare ta. Idan ta samu ciki sai abin da aka
samu ya zama Mukhannas, wato ɗan aljani[9].
·
Idan mace ko namiji na kwana shi kaɗai a ɗaki.
8.0 Alamomin Shigar Namijin
Dare ga Mace ’Yar Adam
Akwai alamomi
da masu ruƙiyya suka fitar wajen gano Namijin
dare ga mace. Alamomin kuwa kashi biyu ne; akwai bayyanannun alamomi, akwai
kuma ɓoyayyu.
8.1 Bayyanannun
Alamomi
Bayyanannun alamomi a nan na nufin ciwon gaɓoɓin jiki ko na
zuciya, waɗanda
suka bayyana a cikin maras lafiya.
i)
Ta riƙa
jin matsanancin ciwon kai kullum.
ii)
Ta riƙa samun yawan faɗuwar gaba.
iii)
Ta riƙa jin ba ta son zama gidan
miji, ko jin ɓacin rai
wanda babu dalili.
iv)
Ta riƙa jin ciwon kwankwaso ko ƙuncin ƙirji.
v)
Ta riƙa jin ciwon mara a kai-a
kai.
vi)
Ta riƙa fama da rashin isasshen
barci ko yawan farkawa cikin dare, kuma
cikin tsoro.
vii)
Rashin tsayar da miji idan ba ta da aure, kuma ga mabiɗa na zuwa wurinta.
viii)
Daɗewa ba ta yi aure ba idan
budurwa ce.
ix)
Yawan mutuwar aure, ta kasa tsayawa ga miji ɗaya. Idan aka ga haka ga mace, ƙari
da wasu alamomi, to ana tuhumar tana tare da namijin dare
x)
Ta zama mai wabi (yawan mutuwar
‘ya’ya tun suna ƙanana
tsakanin shekara ɗaya zuwa biyar).
xii)
Yawan zubar jinin haila a kai - a kai, musamman lokacin da namijin dare
zai sadu da ita.
xiii)
Rashin haihuwa.
8.2
Ɓoyayyun Alamomi
Ɓoyayyun alamomi a nan na
nufin abubuwan da ke wakana cikin duniyar mafarki, da za a iya gane namijin
dare ga mace, kamar mace:
i)
ta riƙa ganin wani yana saduwa da
ita a cikin mafarki.
ii)
ta riƙa ganin ana ba ta jarirai,
kamar ta haihu a cikin mafarki.
iii)
ta riƙa ganin kamar ana taron
buki a cikin mafarki.
iv)
ta riƙa
mafarkin tana cikin ruwan teku ko gulbi.
v)
ta riƙa ganin wasu dabbobi a
cikin barcinta, kamar raƙumi, ko
sa, ko macizai.
9.0 Alamomin
Macen Dare ga Namiji Ɗan
Adam
Kamar yadda mace ’yar Adam ke fama da namijin dare
haka shi ma namiji ɗan Adam ke fama da macen dare. Kuma alamomin da ake gane haka kusan
duk ɗaya ne da na mace, illa
wasu ’yan bambance-bambance da ake samu na halitta. Saboda haka, shi ma
alamomin sa kashi biyu suke wato bayyanannun alamomi da ɓoyayyun alamomi:
9.1 Bayyanannun Alamomi
Bayyanannun alamomi a nan na nufin ciwon gaɓoɓin jiki ko na
zuciya. Idan mutum ɗan
Adam yana fama da cutar iskan dare
zai haifar da samuwar waɗannan
cututtuka:
i) Mutuwar mazakuta ko rauninta.(Rashin tashin
gaban namiji.
ii) Rashin son aure ko jinkirinsa, na tsawon
shekaru masu yawa.
iii) Rashin sha’awar mace.
iv) Saurin samun biyan buƙata wajen jima’i.
v) Rashin haihuwa.
9.2 Ɓoyayyun Alamomi
Ɓoyayyun alamomi a nan na
nufin abubuwan da ke wakana cikin duniyar mafarki, da za a iya gane macen
dare ga namiji, kamar namiji:
i)
ya riƙa ganin yana saduwa da wata
mata a cikin mafarki.
ii)
Ya riƙa ganin kamar ana taron
buki a cikin mafarki.
iii)
ya riƙa mafarkin yana cikin ruwan
rafi ko tabki.
iv)
ya riƙa ganin wasu dabbobi a
cikin barcinsa, kamar raƙumi, ko
sa, ko macizai.
Waɗannan alamomin da aka zayyana ba su kaɗai ne ba, illa su suka fi bayyana ga mai wannan matsalar.
Sannan kuma ba sai duka alamomin sun taru sun bayyana a lokaci guda ba. Wani
lokaci ɗaya daga
cikin alamomin zai iya gamsar da malaman da ke wannan aikin su tabbatar da cewa
lalle akwai namijin dare ko macen dare ga maras lafiya.
10.0 Hanyoyin Warkar da Cutar Namijin
Dare ko Macen Dare
Hausawa na cewa: “Kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi.”
Hanyoyin da Hausawa kan bi wajen warkar da cutar namijin dare ko macen
dare sun kasu kashi biyu; akwai hanyar girka da ’yan bori kan bi da kuma
hanyar ruƙiyya da malaman ruƙiyya ke bi.
10.1 Hanyar
Girka
Girka wata hidima ce da ‘yan bori ke gudanarwa ga marar lafiyar da suke
ganin ta iskoki ce. Gudanar da aikin girka ga marar lafiya na nufin ko dai
iskokin su fita daga jikinsa ya samu lafiya, ko kuma a girke su ga jikinsa su
zauna cikin salama, ba tare da cutar da shi ba, amma tare da yarda da bin ƙa’idojin da za su ɗora masa ga rayuwarsa.
Bayanin yadda ake gudanar da girka ya gabata a wasu ayyuka.[11]
10.2 Hanyar Ruƙiyya
Hanyoyin da malaman ruƙiyya suke bi suna warkar da cutar namijin dare ko macen
dare na da matakai guda uku.
1.
Mataki na farko shi ne ƙoƙarin gano alamomin da aka yi bayani na bayyanar namijin
dare ko macen dare. Idan alamomin sun tabbata, za su gudanar da ruƙiyya ga maras lafiya kamar yadda sukan yi ga sauran
cututtukan da suka shafi iskoki[12].
2.
Mataki na biyu shi ne gabatar da wasu ayyuka da karance-karance ga maras
lafiya. Malam Usamah[13], daga daga cikin malaman ruƙiyya ya tabbatar da cewa, namijin dare ko aljanin
soyayya shi ne mafi haɗari da sharri cikin nau’o’in aljannu. Kuma mafi tsanani ga riƙe jikin ɗan Adam. Bisa ga haka ya fitar da wasu matakai na musamman, waɗanda idan mai wannan cutar ya kula da su, to insha Allah
zai rabu da matsalar gaba ɗaya. matakan su ne:
i)
Ya riƙa
sauraren ko karanta Surar baƙara,
da Surar Nur, da ayoyin Suratul
Yusuf (23-43), da wasu rukunin ayoyin da ake kira
‘ayoyin ƙuna da azaba’ da ‘ayoyin tsoro’ da ‘ayoyin
Muhibba’, kullum sau uku a wuni.
ii)
A karanta Sura Ar-Rahman a cikin ruwan da ke isa wankan tsarki, sannan
a rubuta surar a allo a wanke rubutun
cikin ruwan, sai a yi wanka da ruwan ranar Juma’a. Za a yi wankan a wurin da
babu najasa.
iii)
Maras lafiya zai kula da shafe mahaɗar gaɓɓan jikinsa duka da turaren Almisk baƙi, lokacin shiga barci.
iv)
Maras lafiya zai kula da azkar, wato addu’o’in tsari na safe da
yamma, da na shiga gida da na fita gida, da na shiga barci da sauransu, domin
samun cikakkiyar nasara.
3.
Bayan ɗaukar waɗannan matakai na sama, to dole ne maras lafiya ya yi ƙoƙarin kiyaye
dokokin Allah da nisantar saɓon Allah. Allah ya kare mu, amin.
11.0 Naɗewa
Hulɗa tsakanin Iskoki da Hausawa daɗaɗɗiya ce tun lokacin da suke cikin addininsu na gargajiya. Har bayan samun
wayewar kai da bayyanar addinin Musulunci a ƙasar Hausa, wannan hulɗa ta ci gaba da wanzuwa. Daga cikin irin wannan hulɗar akwai ta ƙiyayya da
ta tsoro da kuma ta ƙauna. Hulɗar ƙauna tsakanin
iskoki da mutane ita ke haifar da namijin dare ko macen dare.
Wannan ya nuna a fili cewa, iskoki na iya auren ’yan Adam kuma suna
sha’awar su. Kodayake ’yan bori da
malaman ruƙiyya sun tabbatar da
yiyuwar saduwa (jima’i) tsakanin ɗan Adam da iska, amma Shari’ar Musulunci ta ƙyamaci irin wannan saduwar, saboda illolin da ke tattare
da shi da kuma cutarwa ga ’yan Adam. Suturce jiki da yawan karanta Alƙur’ani da addu’o’i su ke magance matsalar namijin dare
ko macen dare. Da fatan Allah ya kare mu.
MANAZARTA
ABDULLAHI,
I.M. (Babu Shekara), Fitar da Aljani Daga Jikin Ɗan Adam Ta Hanyar Alƙur’ani (Ruƙiyya). Ɗan fodiyo
Islmic Health Center, Dorayi Karama Kano.
ABUBAKAR,
S.Y. (1997), "Bori A Zariya," Kundin digiri na biyu (M.A), Sashen
Koyar da harsunan Nijiriya, Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya.
AL’IWADIY,
U.M. (Babu Shekara) “Alminhajil Ƙur’aniy Fi
Ilajis Sihir Wal Massis Shaiɗaniy”. Darul Kalimatut
Tayyib. Misra.
ASSHABLI,
A.B.(1985), Akamul
Murjan Fi
Ahkamul Jaan
. Matabatus Sa’i Madina, Sa’udiyyah.
BUNZA, A.M.(1990), “Hayaki Fid Da Na Kogo”. Kundin digri
na biyu (M.A.), Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano.
BUNZA,A.M. (2004), “Magana da Iskoki ta Bakin
Dokinsu”. Muƙala da aka gabatar a taron ƙarawa juna sani na 6 kan Nazarin Harshe da Adabi da
Al’adun Hausawa. Cibiyar Nazarin Harsunan
Nijeria, Jami’ar Bayero Kano.
BUNZA, A.M.
(2005), Boruƙiyyah: Tazarar Bori da
Ruƙiyya a Idon Manazarta
Takardar da aka gabatar a taron tattaunawa da ƙara wa juna sani na
musamman da Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya Jami'ar Bayaro, Kano
ta shirya kan
"Bori" da "Ruƙiyya".
BUNZA, A.M. (2006),Gadon Feɗe Al’ada. TIWAL LTD, Lagos, Nigeria.
CHEDI, Y.F. (Babu shkara), Garkuwan Ɗan Adam
Daga Sharin Shaiɗanu da Matsafa, Rukhsa Publications. Zariya.
Gobir, Y.A (2002) “Iskoki a Idon ‘Yan bori da Masu
Ruƙiyya”. Kundin digiri na biyu, Jami’ar Usamu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
GUMMI,
A.M.(1982), Tarjamar Ma’anonin Alkur’ani Mai Girma. Darul Arabia, Lebanon.
IBRAHIM,
S.M. (1982), “Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci Kan Hausawa”
Kundin Digiri Na Biyu Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
MAHMUD,
A.M. (Babu Shekara), Hanyoyin Waraka daga Cutar Aljannu da Sammu. Burji Publishers & Co.
Kano.
MAHMUD,
A.M. (1997), Hanyoyin Gane Sihiri da Warware Shi, Burji Publishers &
Co. Kano.
MUHAMMAD
S.U. da sauransu, (Babu Shekara), Alaƙar Aljannu
da Dan Adam. J.I.B.W.I.S.,
Bagaren Shaikh Ismaila Idris Jos Reshen Kano.
SULAIMAN,
U.F. (2000) ’Muhimman Bayyanai a kan Asiran Aljannun,. Al-Ameen Press. Kofar Atiku,
Sokoto.
SULAIMAN,
U.F. (2000), Fassara ‘Bayyanar da Gaskiya a kan Shigar Aljani Cikin’, Jikin
Mutum da Raddi ga wanda ya yi Masu, na Shaikh ABDULLAHI Bin Baez. Daylight
Foundations, Sokoto.
WAHID,
A.B. (1988), Wiƙayatul Insana Minal Jinn Was Shaiɗan. Darul Bashir Alkahira (Misra).
[1]
Don karin
bayani a kan
ma’anar ruƙiyya
da yadda ake yin ta, dubi: Gobir, Y.A (2002) “Iskoki a Idon ‘Yan
bori da Masu Ruƙiyya”. Kundin digiri na biyu,
Jami’ar Usamu Ɗanfodiyo,
Sakkwato.
[2]
Don karin
bayani a kan
ma’anar ruƙiyya
da yadda ake yin ta, dubi: Gobir, Y.A (2002) “Iskoki a Idon ‘Yan
bori da Masu Ruƙiyya”. Kundin digiri na biyu,
Jami’ar Usamu Ɗanfodiyo,
Sakkwato.
[3] Don karin
bayani sauran sunayen iskoki dubi: lamba ta 1, da Bunza A.M.
(2006)Gadon Feɗe
Al’ada. TIWAL LTD.
[4] Don
ƙarin bayani dubi Aliyu Muhammad
Bunza: “Magana da Iskoki
ta Bakin Dokinsu”. (2004). Muƙala
da aka gabatar a taron ƙara
wa juna sani na 6 kan
Nazarin Harshe da Adabi
da Al’adun Hausawa. Cibiyar
Nazarin Harsunan
Nijeria, Jami’ar
Bayero Kano.
[5] Don ƙarin bayani:
Dubi Aliyu
Muhammad Bunza:
Boruƙiyya: Tazarar
Bori da Ruƙiyya a Idon Manazarta
Takardar da aka gabatar a taron tattaunawa da ƙara
wa juna sani na musamman da Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya Jami'ar Bayaro, Kano ta shirya kan
"Bori" da "Ruƙiyya", ranar 19 ga Maris,
2005.
[6] Don ƙarin bayani dubi Badarud din Abdullahi Asshabli (1985) Akamul Murjaan Fi
Ahkaamil Jaan.
Maktabah
Ibn Sina, Misra, Alƙahirah. Shafi na 77 – 89.
[7] Dubi
lamba ta 7, shafi na 78.
[8]
Iliyasu (2000) ya
tabbatar da haka, sun yi wata mata ruƙiyya
a Sakkwato, aljanin ya ce ya shige ta ne tana tsiraice bayan ta ba shi sha’awa.
[9]
An yi ruƙiyya a Sakkwato ga matar da
ke da wani jinjiri lagwas kamar ba ya da ƙashi
a jikinsa, aljanin ya ce ɗansa
ne, sai an ba shi abinsa zai fita. Da aka ce an ba shi jinjirin, cikin dare ya
zo ya ɗauke shi ana
barci, sai uwar ta samu lafiya.
[10]
Likitoci asibitocin
zamani sun tabbatar da haka. A hirar da na yi da wani ƙwararren likita Dr. Yakubu Ahmad na Asibitin Koyarwa ta Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sakkwato,
ranar Alhamis 13/11/2008, ya tabbatar da cewa mafiyawan zubar cikin mata daga
aljani ne.
[11]
Bayanin
yadda ake girka dubi: Aliyu Muhammad Bunza (1990),
“Hayaki Fid Da Na Kogo”. Kundin digri na biyu (M.A.), Sashen
Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero Kano,
da Gobir,
Y.A (2002) “Iskoki a Idon ’Yan bori da Masu
Ruƙiyya”.
Kundin digiri na
biyu, Jami’ar Usamu Ɗanfodiyo, Sakkwato.shafi na 92.
[13]
Usamah Muhammad
Al’iwadiy (Babu Shekara) “Alminhajil Kur’aniy Fi
Ilajis Sihir Was Massis
Shaidaniy”. Darul Kalimatut
Tayyib. shafi na 62 -99.
No comments:
Post a Comment