Monday, December 31, 2018

Tubalan Iskoki a Ginin Littafin Ruwan Bagaja



Nazarin hikimomin al’adun Hausawa da harshensu kullum sai ƙara bunƙasa yake yi saboda irin ƙoƙarin da masana da ɗaliban Hausa ke yi na rayar da su. Adabi kuwa, rumbu ne da ake hango rayuwar kowace irin al’umma da iri-iren abubuwan da take cuɗanya da su a rayuwarta. Saboda haka, dangantaka tsakanin al’ada da adabi, aba ce mai ƙarfin gaske, tamkar harshe ne da haƙori. Masana sun tabbatar da cewa al’ummar Hausawa sun daɗe suna hulɗa da iskoki, kuma hulɗar, ta samo asali ne tun lokacin da suke cikin addininsu na gargajiya. Maƙasudin wannan muƙala shi ne hango wani babban gurbi a cikin al’adar Bahaushe, wato yadda iskoki suka mamaye tunanin Bahaushe, har aka wayi gari, da wuya ya faɗi, ko ya rubuta, wata fasaha ko hikima, ba tare da ya saka iskoki a ciki ba. Hasali ma, saka iskokin shi ke haskaka fasahar da ya rubuta, kamar yadda littafin Ruwan Bagaja zai tabbatar.

Yakubu Aliyu Gobir
Tsakure
Nazarin hikimomin al’adun Hausawa da harshensu kullum sai ƙara bunƙasa yake yi saboda irin ƙoƙarin da masana da ɗaliban Hausa ke yi na rayar da su. Adabi kuwa, rumbu ne da ake hango rayuwar kowace irin al’umma da iri-iren abubuwan da take cuɗanya da su a rayuwarta. Saboda haka, dangantaka tsakanin al’ada da adabi, aba ce mai ƙarfin gaske, tamkar harshe ne da haƙori. Masana sun tabbatar da cewa al’ummar Hausawa sun daɗe suna hulɗa da iskoki, kuma hulɗar, ta samo asali ne tun lokacin da suke cikin addininsu na gargajiya. Maƙasudin wannan muƙala shi ne hango wani babban gurbi a cikin al’adar Bahaushe, wato yadda iskoki suka mamaye tunanin Bahaushe, har aka wayi gari, da wuya ya faɗi, ko ya rubuta, wata fasaha ko hikima, ba tare da ya saka iskoki a ciki ba. Hasali ma, saka iskokin shi ke haskaka fasahar da ya rubuta, kamar yadda littafin Ruwan Bagaja zai tabbatar.
Gabatarwa
            Masana al’ada da tarihi na ganin, hikima da tunanin mutane da ke bayyana a adabinsu na baka, da rubutacce wata fitila ce, ta ƙyallaro al’adun rayuwarsu da yadda suke more mata. Saboda haka, dangantaka tsakanin al’ada da adabi, aba ce mai ƙarfin gaske, kamar harshe ne da haƙori. Nazarin al’ada cikin adabi ko adabi cikin al’ada abu ne da masana tuni suka hange shi (Abdullahi 2000). Maƙasudin wannan takarda shi ne, fito da wani babban gurbi a cikin al’adar Bahaushe, wato iskoki a matsayin babban tubali wajen gina ƙagaggen labarin littafin Ruwan Bagaja. Ƙagaggen labari wani nau’in rubutaccen adabin Hausa ne da ya haɓaka bayan zuwan Turawan mulkin mallaka, a sanadiyyar kafa wasu hukumomin samar da littattafan karatun Hausa a makarantun boko. Duk da yake, muƙalar a kan ƙagaggen labari ne, da gangan ta kauce wa, duba tarihin ƙagaggun labarai da nau’o’insu, saboda sun gabata a wasu ayyuka (Yahaya, 1988 da Malumfashi, 2006/2009/2010/2011 da Bakura, 2011 da Adamu, 2013). Da farko, muƙalar ta fayyace ma’anar fitillun kalmomin  matashiyarta domin share fagen nazarin.

Iskoki a Tunanin Hausawa
          ‘Iskoki, kalma ce mai nuna jam’i na ‘iska’, wadda ƙamusoshin Hausa zuwa Hausa, suka ba ta ma’ana kamar haka: Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero, Kano, ya ba ta ma’anar ‘Mutanen ɓoye’. Shi kuwa Calvin Y. Garba[1], ya ba ta ma’anar ‘Rahwani, musamman na bori’. Waɗannan ƙamusoshi sun bayar da ma’anar iska ne a matsayin kalma kawai, ba ma’ana ta ilimi ba. Bisa ga haka, ga abin da masana ke cewa:
Iskoki a wajen Bahaushe wasu halittu ne masu kama da mutane ta fuskar halittarsu, da surarsu, da ayyukkansu, da al’adunsu, da ɗabi’unsu, da harshensu, da siyasar rayuwarsu, da dai makamantansu. (Bunza, 2006:1)

            A nan, Bunza yana son ya tabbatar da imanin Bahaushe dangane da iskoki  cewa, su ma halittu ne kamar mutane. Masu ayyuka da sunaye irin na mutane. Duk da yake ba mutane ba ne, za a iya fahintar haka tun daga irin sunayen da yake kiran su da shi. Misali, Bahaushe ya kira su ‘iskoki’ ne domin ba ya ganin su kamar yadda ba ya ganin iskan da yake shaƙawa. Yana kiran su ‘Masu abu’ don suna nuna isa ga duk abin da suka nufi aikatawa ko suke buƙata. Yana kiran su ‘Mutantani’ saboda sun yi tarayya da mutane ta ɓangaren jinsi da hali.
            Masana al’adun Hausawa irin su Greenberg (1946), Besmer (1973), Ibrahim (1982), Bunza (1990/2006), Ismaila (1991), da sauransu, sun yi rubuce-rubuce da dama a kan iskoki da matsayinsu a rayuwar Bahaushe. Magabata sun tabbatar da imanin Bahaushe a kan samuwar iskoki. Haka kuma sun tabbata ba a ganin su. Hausawa sun yi imani iskoki buwayayyi ne, masu ban tsoro, masu ƙarfi a kan mutane, kuma masu iya cuta musu. Bayan bayyanar Musulunci a ƙasar Hausa cikin ƙarni na 14 - 15, Hausawa suka fara amfani da sunaye irin su: Aljani, da Ira'izzai, da Jinnu, da Rafani, da Shaiɗani, da dai makamantansu. Dalili kuwa shi ne, waɗannan sunayen sun zo cikin nassoshin littattafan addini, waɗanda suka haɗa da Alƙur'ani da Hadisai da sauran litattafan Furu'a da na Tauhidi da na Adabi (Bunza, 2004:4-5). Bisa ga haka, addinin Musulunci ya yi tasiri ga sunayen iskoki da Bahaushe ke amfani da su a yau. Don haka, sunayen da yake amfani da su na Hausa, suka rafashe, sai a bakunan bokaye da 'yan bori, saboda kusancinsu da bori da tsafi[2]. Wannan, ya tabbatar da daɗaɗɗiyar hulɗa tsakanin iskoki da Hausawa tun ga addininsu na gargajiya da samar da waraka daga cutuka. Watakila, wannan ya sa aka kawo bayanin neman waraka daga ciwon Yarima ɗan sarki da Ruwan Bagaja a cikin labarin, yana cewa a shafi na 5:
Ina nan wata rana an taso daga Juma’a, sai na ga Liman babana ya dawo gida idanu sharaf sharaf da hawaye. Na tarye shi da kuka, na ce, “Baba, lafiya?” Ya ka da baki ya ce, “Ina lafiya, yau Sarki ya muzanta ni cikin taro?” Wai don yau ana cikin fadanci, ya ce ɗansa Yarima ba ya da lafiya, sai a kwantar a tayar. Ni kuwa na ce na ji an ce da za a sami Ruwan Bagaja a wani gari, da mutanen garin nan duk sun huta da masassarar zamani. Daga wai na faɗi ’yar wannan, sai Sarki ya harzuƙa, ya ce wai ba’a nake jan shi da ita. Ya  ce wai in ba shegantaka ba, da shaƙiyancin da na saba, ina na taɓa ganin wanda ya sami Ruwan Bagaja a duniya?

Rabe-raben Iskoki
            Masana tarihi da al’ada sun yi bincike game da rabe-raben iskokin da Hausawa ke mu’amula da su wajen neman biyan bukata. Ibrahim (1982), ya raba iskoki kashi biyu ta fuskar ɗabi’a: ‘Farare’ da ‘Baƙaƙe’. Fararen su ne masu kirki, masu taimakon mutane, ba su son dukiya ko sarauta. Suna bayar da maganin cuce-cuce, ciki har da na ‘baƙaƙen’. Baƙaƙen kuwa su ne, maƙetata, masu neman mutum da sharri, kamar a yi wa wani magani ya mutu ko ya sami taɓin hankali, da sauransu.
            Bunza (2006:9-10), ya kalli rabe-raben iskoki  ta fuskar halitta da ɗabi’arsu. Duk da kasancewar Bahaushe ya yi imani cewa sifar iskoki ta halitta ta bambanta da ta ɗan Adam, amma ya yarda cewa, suna da jinsin mata da maza. Ta fuskar shekaru kuma, ya yarda cewa akwai yara matasa da manya da kuma tsofaffi. A tsarin tunaninsu kuwa, ya yarda suna da masu hankali cikinsu, akwai kuma mahaukata.
            Haka su ma malaman Ruƙiyya, sun kasa aljannu gida biyu: Akwai Musulmi akwai kuma Kafurai, akwai masu sauƙin kai ga mu’amula akwai kuma masu taurin kai. A cikin labarin littafin Ruwan Bagaja, an yi amfani da aljannu masu kirki, kuma Musulmai, kamar yadda ya zo a shafi na 16, yana cewa:
Sai na diro daga jirgi wai in faɗa ƙasa. Da faɗawata sai na nutse, na yi ƙasa! Abin ikon Allah sai na isa wani gida a ƙasan tabkin, na tarad da waɗansu irin mutane masu manyan kawuna. Ashe ’yan ruwa ne. Suka yi maraba da ni. Bayan na huta, suka tambaye ni labarina, duk na kwashe na faɗa musu. Da suka ji haka, sai suka ji tausayina, suka ba ni magani, idona ya warke. Sarki ya sa aka kai ni tudu, aka sa ni hanya.

            Haka kuma, aljannun da aka yi amfani da su aka gina labarin, an nuna Musulmai ne, saboda an yi amfani da kalmomin ƙissar Annabi Sulaiman da Babansa Annabi Dawud, a cikin Alƙur’ani Maigirma. Shafi na 36 yana cewa:

Ina cikin ramin nan, ina jiran mutuwa, sai na ga waɗansu aljannu guda biyu sun ɗauko wani ɗan’adam. Suka sauke shi nan kusa da ni kaɗan, suka tona rairayi kamar shan ɗaki. Sai na ji babban ya ce, “Bi hurmati Sulaimanu Ibnu Dawuda, iftah!” Sai na ga ƙasa ta buɗe, suka shiga da mutumin nan.

            Haka kuma, ta fuskar yanayin wurin zaman su, ko kuma inda suke rayuwa, ana iya kasa iskoki zuwa kashi biyu kamar haka: iskokin tudu da na ruwa: Iskokin tudu su ne iskokin da ke zama a farfajiyar sararin duniya, ko a cikin gari ko a dokar daji, ko gindin itatuwan da aka zayyana a baya, da sauran wurare da aka ambata. Ana samun ’yan kaɗan daga cikinsu masu kirki, amma masu sharri sun fi yawa. Ta fuskar rikiɗa kuwa, sukan rikiɗa su koma irin sifar mutane ko dabbobin da suke tare da su, kamar su dawaki da raƙumma, da shanu da tumaki, da alfadari,  da jakuna, da sauransu. Iskokin ruwa kuwa, su ne iskokin da ke zama a cikin ruwan teku ko na rafi ko na gulbi, ko kududdufi, da sauransu. Sukan fito waje a sararin duniya ɗan lokaci, sannan su koma inda suke rayuwa, wato cikin ruwa ko kuma can ƙasan ruwan teku. Wannan ya sa Bahaushe ke kiran su ’Yan ruwa. Kamar yadda iskokin tudu ke rikiɗa, haka su ma iskokin ruwa kan rikiɗa su koma irin dabbobin ruwa, kamar su kada, ko tsari, ko dorina, ko kifi, da sauransu. Ta fuskar mugunta kuwa su ma kamar na tudu suke. Akwai na ƙwarai kaɗan, sannan mafi yawa daga cikinsu miyagu ne, sukan cuta wa ‘yan Adam, musamman waɗanda suka shiga ruwa don wata lalura ko tsallakawa.
            Dangane da labarin littafin Ruwan Bagaja kuwa, an gina labarin ne da nau’in iskokin ruwa (’Yan ruwa), kamar yadda aka faɗa a littafin, a shafi na 6-7:
Ruwan Bagaja dai akwai shi a duniya, amma yana hannun aljannu. Ƙarewa ma ba shi a bisa ƙasan nan da muke takawa.

Aljannun da ke kula da rijiyar Ruwan Bagaja, suna can ƙasan tsakiyar teku ne, lokacin da Imam ya ga wasu aljannu sun zo wurin, sun yi addu’a, ƙasa ta buɗe suka shiga. Yana cewa a shafi na 36:
Suka sauke shi nan kusa da ni kaɗan, suka tona rairayi kamar shan ɗaki. Sai na ji babban ya ce, “Bi hurmati Sulaimanu Ibnu Dawuda, iftah!” Sai na ga ƙasa ta buɗe, suka shiga da mutumin nan. Ni kuwa na yi bulum na sha jinin  jikina, duk na rufe jikina da rairai wai na yi wa kaina kabari, shi ya sa Allah bai ba su ikon ganina ba. Can sai na ga sun fito, sun ce, “Bi hurmati Sulaiman Ibnu Dawuda, igliƙ!” sai na ga ƙasa ta rufe. Suka mai da rairayin bisa, kamar da ɗai duniya ba kome.

Matsayin Iskoki a Adabin Hausa
          Adabi, wani hoto ko madubi ne da ake iya hango al’ada da hikimomi da fasahar wata al’umma. Haka ma iri-iren abubuwan da take cuɗanya da su a rayuwarta. Daga ciki akwai ɓangarorin siyasa da tattalin arziki da zamantakewa da addini da sauransu. Ta la’akari da yanayin adabin Hausawa, masana sun kasa shi gida biyu: adabin gargajiya da adabin zamani (Ɗangambo, 1984).
            Adabin gargajiya shi ne adabin baka. Ya ƙunshi fasaha da hikimomin da Hausawa suka gada kaka da kakanni. Ya kuma ƙunshi tatsuniyoyi da labarai da almara da tarihi da tarihihi da ƙissa da hikayoyi da kirari da karin magana da waƙoƙin baka da wasannin dandali da camfe-camfe da kacici-kacici da roƙo da ba’a da barkwanci da baƙar magana da sauransu (Malumfashi, 2009:89). Kowane reshe daga cikin rassan adabin baka, aka ɗora a mizanin tubalan gininsa, za a samu iskoki dumu-dumu a ciki. Dalili kuwa, saboda a cikin tunanin tubalan ginin duk wata tatsuniya ko labari ko tarihi ko hikaya da sauransu, ana son a samu burgewa a ciki ko buwaya[3] ko ɗaukaka ko neman maganin wata matsala. Shi kuwa Bahaushe a tunaninsa, duk waɗannan abubuwa ba su samuwa kai tsaye sai da taimakon iskoki. Wannan tunanin ya shiga jinin Bahaushe, ya tashi da shi, kuma ya yi tasiri a rayuwarsa ta ilimi da addini da siyasar zamantakewa. 
            Adabin zamani kuwa, shi ne rubutacce. Ƙunshiyarsa ita ce, ƙarin fasaha da hikimomin da Hausawa suka samu bayan sun iya karatu da rubutu, ko sun shaƙu da wasu al’ummomi, musamman Larabawa da Turawa. Bisa ga haka, Hausawa suka fara rubuta hikimomi da fasahar da suke da su cikin adabin baka. A wajen rubutun, akan samu tasirin adabin baka a cikin rubutun nasu. Domin kuwa, tunani da ƙirƙirar marubuci tare suke tafiya da fasahar harshen da yake rubutu da shi. Harshe kuma shi ne, taskar da ke ɗauke da al’adu da sassan adabin bakan al’umma. Wannan shi ne dalilin da ya sa sassan adabin baka na Hausa suka sami kansu a cikin rubutaccen adabi ta hanyoyi daban-daban: wasu a matsayin tubalai, wasu kuma domin kwalliya irin ta rubutun adabi. Samun sassan adabin baka a cikin rubuce-rubucen ƙagaggun labarai, ya sa aka riƙa samun tubalan iskoki a ciki saboda dalilan da aka ambata a baya. Idan aka duba littattafan ƙagaggun labarai musamman na farko-farko, masu cike da fasaha za a samu haka. Misali, littattafai irin su: Ganɗoki  na Malam Bello Kagara, da Jiki Magayi na Malam Tafida, da Iliya Ɗan Maiƙarfi na Ahmadu Ingawa, da Taurariya Maiwutsiya na Ummaru Dembo, da shi kansa Ruwan Bagaja na Alhaji Abubakar Imam da sauran ire-irensu, duk an gina labaransu da tubalan iskoki.
            Haka kuma, wani dalilin da ya ƙarfafa amfani da tubalin iskoki a cikin rubutaccen adabin Hausa shi ne, samun fahimta makusanciya a kan iskoki tsakanin al'ummar Larabawa da Hausawa. Kasancewar su nesa ga juna a doron ƙasa, al'adunsu ta fuskar yadda suke kallon iskoki ya yi kusa da juna ƙwarai da gaske. Haka kuma, Labarawa suna ɗaya daga cikin al’ummomin farko, masu hanyar karatu da rubutu da Hausawa suka fara cuɗanya da su. Littattafan adabin Larabci cike suke da tubalan aljannu. Misali, Alfu Laila Wa Lailah da Kalilah Wa Dimnah da Rauzul-Jinan da Kitab Nuruz Zaman da Maƙamatul Harir da sauransu. Ƙarawa da ƙarau, sai addinin Musulunci ya zo da cikakken bayani a kan halittar aljannu da halayensu da sauran al’amurran da suka jiɓince su. Misali, akwai sura mai sunan ‘Surar Aljannu’ a cikin Alƙur’ani. Ƙissar Alƙur’ani ta dangantakar Annabi Sulaiman da aljannu ta isa misali babba. 

Iskoki a Littafin Ruwan Bagaja
            Littafin Ruwan Bagaja yana ɗaya daga cikin littattafan da aka rubuta na gasar farko ta rubuta ƙagaggun labaran Hausa da Hukumar Talifi ta shirya a shekarar 1933. Haka kuma, shi ne ya lashe gasar (Yahaya 1988).  An yi nazarin wannan littafi a matakai daban-daban na ilimi ba su da iyaka. Kaɗan daga cikin su akwai na Ingawa (1969) da Yunusa (1985) da Kudan (1987) da Bunza (1991) da Malumfashi (1996, 2009) da dai sauransu. Marubucin Littafin Ruwan Bagaja, wato Abubakar Imam, ya shahara ƙwarai a duinyar Marubuta. Rubuce-rubucensa sun taka muhimmiyar rawa a dandalin nazarin ƙagaggun labaran Hausa a duniya. A fahimtata, idan aka cire Adabin Abubakar Imam daga cikin rubutaccen adabin Hausa, ɗan abin da za a bari bai taka kara.
            A cikin littafin Ruwan Bagaja an samu tasirin sassan adabin bakan Hausa. Misali, an yi amfani da tatsuniyoyin Hausa a matsayin tubalan ginin waɗansu sassa na littafin. Akwai tatsuniyar Ruwan Bagaja, wadda ita ma haka aka gina ta kamar yadda aka gina labarin littafin Ruwan Bagaja, sai dai da ɗan sauyi. Akwai kuma tatsuniyar Gizo da Tsuntsaye, inda Gizo ya faɗo ruwa ya gamu da ‘yan ruwa (iskokin ruwa), ta taimaka wajen gina zaman Alhaji Imam a Ɗandago da yadda ya daɗa kogin Ƙaruna ya gamu da ‘yan ruwa. Haka kuma, an ɗauko tatsuniyar Gizo da amaryarsa da ta Gizo da Sarki[4], don su taimaka wajen gina waɗansu sassa na littafin, musamman a zaman Alhaji Imam a wani gari, Baku da wani Zango da ƙasar Hindu da kuma zamansa a gidan Sarkin Gardi (Malumfashi, 2009:89-90). Duk waɗannan tatsuniyoyi suna ɗauke da tubalan iskoki a cikinsu.
            Bayan haka, tubalan iskoki sukan shigo a cikin labari don a nuna burgewa da buwaya ko ɗaukaka ko kuma neman magani. Littafin Ruwan Bagaja, tun daga farko, an nuna saƙon wannan muƙalar, domin Ruwan Bagaja ruwa ne da ake magani da su ga wata cuta mai wuyar magani, shi ya sa aka nuna ruwan ga hannun aljannu suke. Ya fara fito da maganar tun a shafi na 5, inda babansa Liman ya dawo daga fadar Sarki. Yana kuka, ɗansa Imam ya tambaye shi me ya faru? Sai ya ce:
Wai don yau ana cikin fadanci, ya ce ɗansa Yarima ba ya da lafiya, sai a kwantar a tayar. Ni kuwa na ce na ji an ce da za a sami Ruwan Bagaja a wani gari, da mutanen garin nan duk sun huta da masassarar zamani. Daga wai na faɗi ’yar wannan, sai Sarki ya harzuƙa, ya ce wai ba’a nake jan shi da ita. Ya  ce wai im ba shegantaka ba, da shaƙiyancin da na saba, ina na taɓa ganin wanda ya sami Ruwan Bagaja a duniya?

            Har ila yau, Imam ya ci gaba da bijiro da yadda za a yi ya samu Ruwan Bagaja da inda zai same su. Ya nemi tsohon da ya tarar a cikin kogon dutse da ya buga masa ƙasa, (wato ya yi masa duba) ya ga ko zai dace da Ruwan Bagaja. Ga abin da ya ce a shafi na 6-7:
Bayan mun saba da juna na ce masa ya buga min ƙasa, ya gaya mini labarina da labarin niyyata. Ya buga ƙasa, ya ce, “Ruwan Bagaja dai akwai shi a duniya, amma yana hannun aljannu. Ƙarewa ma ba shi a bisa ƙasan nan da muke takawa.

Imam ya fara haɗuwa da ’yan ruwa a lokacin da ya diro daga jirgi da nufin ya sauka ƙasa. Kwatsam! ya ji shi a nutse cikin ruwa, sai ga shi tare da ’yan ruwa, yana cewa, a shafi na 16:
Ko da na ji haka, sai na ce, “Yau ga yaran banza, sun dai mai da mutane makafi. Ai na san mun kawo.” Sai na diro daga jirgi wai in faɗa ƙasa. Da faɗawata sai na nutse, na yi ƙasa! Abin ikon Allah sai na isa wani gida a ƙasan tabkin, na tarad da waɗansu irin mutane masu manyan kawuna. Ashe ’yan ruwa ne. Suka yi maraba da ni. Bayan na huta, suka tambaye ni labarina, duk na kwashe na faɗa musu. Da suka ji haka, sai suka ji tausayina, suka ba ni magani, idona ya warke. Sarki ya sa aka kai ni tudu, aka sa ni hanya.

            An sake kawo maganar aljannu a shafi na 20. Sai dai a nan, ba a matsayin tubali ba. A matsayin kwalliya ga labarin. Domin haukan ƙarya ne aka yi, da sunan aljannun ƙarya sun taɓa shi. Buƙata ya samu kuɓuta daga hannun sarki a kan abin da Zurƙe ya yi masa, na tura shi ɗakin matar aure cikin dare. Don haka ya yi tabarmar kunya, ya ce turo shi aka yi. Kuma ya ɗauki haukan ƙarya don ya kuɓuta. Ga abin da yake cewa:
Kowace tambaya ya yi mini, sai in ce, “Haka aka yi.” Sai ya ce, “Na san a rina! In ba motsattse ba wa zai faɗa ɗakin wani ya ce wai turo shi aka yi? Lalle aljannunsa suka turo shi.” Ya sa aka kai ni gidan mahaukata aka sa a turu. Da Wazirin garin ya ji labari ya ce ƙarya nake yi. Lafiya ta lau!. Saboda haka Sarki ya taho gidan mahaukata, bayan an kwana bakwai, wai don ya jarraba ni. Ya sa aka kira ni, ya ce, “Ina sunanka?” Na ce, “Mai ’Yangabas.”

            An ci gaba da gina labarin da tubalan aljannu a shafi na 35. Imam ya isa wani gari mai suna Baitul Maƙaddas. Ya sauka gidan sarki, kuma ya nemi sarki da a tara masa tsofaffin mutane su ba shi labarin ko akwai wanda yake da labarin Ruwan Bagaja? Yana cewa:
Sa’an nan aka kira wannan tsohon, aka ce ya ba da labarin. Ya ce, Ruwan Bagaja dai yana cikin ƙasar Irami ne, ƙasar Irami kuwa ƙasa ce ta aljannu. Ruwan Bagaja kuwa ma ba nan ƙasar yake ba, yana can bisa wani dogon dutse da ake kiransa Dutsen Ƙaf. Babu mahalukin da yake iya zuwa can sai aljannu, ko aljannu ma sai masu fikafikai kaɗai. Amma na mance sunan rijiyar yanzu. Ko aljani ya yi ƙoƙari ya isa dutsen nan kafin ya ɗebi ruwan sai wani ikon Allah. Akwai waɗansu maridai, masu jiran rijiyan nan, kuma akwai waɗansu ’yan karance-karance kuma da ake yi kafin a sami damar shiga. Akwai kuma dokoki da ake bi in an shiga, da cewa mutum  ya kuskure ɗaya daga cikinsu sai a yi ban da shi. Ko kakan namu ma ya manta da waɗannan dokokin da addu’o’in. Ka ji abin da na na sani na labarin Ruwan Bagaja, ranka ya daɗe!”

            Imam ya samu labarin Ruwan Bagaja na ƙasar Aljannu da ake kira Iram. Bisa hanyarsa ta isa Iram, jirginsu ya yi karo ya nutse, kowa ya halaka sai shi kaɗai ya tsira. Ya samu kansa a kan wani tsibiri tsakiyar teku. Yana tunanin mutuwa ta zo masa, sai ya tona yashi ya yi rami ya shige a ciki yana jiran mutuwa. Ga abin da yake cewa a shafi na 36:

Ina cikin ramin nan, ina jiran mutuwa, sai na ga waɗansu aljannu guda biyu sun ɗauko wani ɗan’adam. Suka sauke shi nan kusa da ni kaɗan, suka tona rairayi kamar shan ɗaki. Sai na ji babban ya ce, “Bi hurmati Sulaimanu Ibnu Dawuda, iftah!” Sai na ga ƙasa ta buɗe, suka shiga da mutumin nan. Ni kuwa na yi bulum na sha jinin  jikina, duk na rufe jikina da rairai wai na yi wa kaina kabari, shi ya sa Allah bai ba su ikon ganina ba. Can sai na ga sun fito, sun ce, “Bi hurmati Sulaiman Ibnu Dawuda, igliƙ!” sai na ga ƙasa ta rufe. Suka mai da rairayin bisa, kamar da ɗai duniya ba kome.

            Imam ya fara ganin hasken biyan bukatarsa na samun Ruwan Bagaja. Domin kuwa, ya samu kutsa kai ƙarƙashin ruwa ta hanyar jin adu’ar da aljannu suka yi, shi ma ya yi , ƙofa ta buɗe ya shiga. Bayan ya shiga, kuma abin da ya gudana tsakaninsa da Saƙimu, ya kiciɓis da takobin zinari, wanda yake da bawa aljani. Yana shafa[5] takobin cikin rashin sani, sai wani aljani ya fito. Ga abin da ya ce masa a shafi na 36-37:
Faɗi bukatarka ya ubangijina!... Ni ne bawan takobin nan. Yafisu ɗan Nuhu ya ajiye ni nan in yi wa takobin nan bauta, don da shi ya yi yaƙi sa’adda yake da rai har ya ƙaura. Da na ji haka, sai zuciyata ta yi fari, na ce, “To, in haka ne, kai ni in samo Ruwan Bagaja. Da jin wannan kalami nawa, sai ya yi ƙara ya ce, “Ba ni da iko!, amma na kai ka wurin wani babbanmu, in ya yarda shi kaɗai ke da ikon wurin duk ƙasan nan. Tun da aka halicci duniya, aka halicci Ruwan Bagaja a nan, don dukan aljannu. Tun lokacin nan kuwa zuriyarsu ke riƙe da ita har yanzu. Da na ji haka sai na ce, to ya kai ni. Kafin ƙyaftada bismilla, sai muka iso wani ƙaton kogo, kusa da babban Birnin Iram. Ya ce, “cikin kogon nan yake!”

Tun daga farkon babi na takwas na wannan littafi, wato shafi na 37 har zuwa ƙarshen littafin, bayani ne na gwagwarmayar ɗebo Ruwan Bagaja. Imam ya sha wahalhalu tsakaninsa da aljannu, har zuwa inda buƙatarsa ta biya. Ya samo Ruwan kuma ya dawo gida lafiya, ta hanyar rijiyar Maiburgami da ke Kano. An kuma ba Yarima ɗan Sarki Ruwan, ya sha, ya samu lafiya, nan take.

          Abubuwan da suka bijiro cikin littafin Ruwan Bagaja a kan zamantakewar al’umma, abubuwa ne da suka dace da wannan lokaci, musamman abin da ya shafi tsafe-tsafen neman kuɗi da mulki da bugun ƙasa, na daga ayyukan malaman budeji da bokaye waɗanda ke haɗa maganinsu da sharaɗin samo wani abu mai wuyar samu. Misali, sukan ce mutum ya nemo gashin gezar zaki, ko kitsen ƙuda, ko ayyana wani abu wanda ba a san inda za a nemo shi ba, amma sai su nuna su, suna iya nemo abin, a ba su kuɗi. Duk da kasancewar littafin ya shekara tamanin (80) da wallafawa, amma saƙon da ke cikinsa ya dace da zamanin yau, musamman ta fuskar rayuwar Hausawa ta yau da kullum.  

Naɗewa
            Littafin Ruwan Bagaja littafi ne da aka gina a kan hikima da fasahar al’ummar Hausawa da ta Larabawa. Al’adun waɗannan al’ummomin guda biyu, ta fuskar yadda suke kallon iskoki sun yi kusa da juna ƙwarai da gaske. Wannan shi ya ba marubucin damar gina labarun da ke cikin littafin da tubalan iskoki. Tun daga harsashen ginin labarin littafin, da iskoki aka fara kuma da su aka yi rufin ginin. An yi ginshiƙai a wurare goma sha biyu da tubalan iskoki a cikin littafin. Amfani da tubalan iskoki ko aljannu ya taimaka ƙwarai wajen isar da saƙon littafin. Da babu tubalan iskoki a cikin ginin labarun, da saƙon littafin bai fito ba. Tubalan iskoki sukan shigo a cikin labari inda ake son nuna burgewa da buwaya ko ɗaukaka ko kuma neman magani. Littafin, tun daga sunansa, an nuna magani ne saƙonsa. Domin Ruwan Bagaja, ruwa ne da ake magani da shi ga wata cuta mai wuyar magani. Shi ya sa aka nuna Ruwan, ga hannun aljannu yake. Babu shakka, bijiro da tubalan iskoki a cikin ginin labarun littafin, ya taimaka masa wajen lashe zaɓen gasar farko, ta rubuta ƙagaggun labaran Hausa da Hukumar Talifi ta shirya a shekarar 1933.

Manazarta
Ahmad, I. A. (1984) “Cututtukan Ciki da Magungunansu.”  Kudin digiri na farko, (B. A. Hausa) Jami’ar Bayero. Kano.
Ɗangambo,  A. (1984) Rabe-Raben  Adabin Hausa  Da Muhimmacinsa Ga  Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph Publishing Company.
Bunza, A. M. (1990), “Hayaƙi Fid Da Na Kogo: (Nazarin Siddabaru Da Sihirin Hausawa)”, Kundin digiri na biyu (M.A. Hausa), Jami’ar Bayero. Kano.
Bunza, A. M. (1991) “Sharhin Ciki da Wajen Littafin Ruwan Bagaja.” Maƙalar da aka gabatar a taron Makon Hausa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo. Sakkwato.
Bunza,  A. M.  (1995) “Magungunan Hausa a Rubuce: (Nazari Ayyukan Malaman Tsibbu),” Kundin digiri na uku (Ph.D. Hausa)  Jami’ar Bayero. Kano.
Bunza, A. M. (2006) Gadon Feɗe Al’ada . Tiwal Nig. Ltd. Lagos.
Gusau, S. M. (2008) Dabarun Nazarin Adabin Hausa. Kano: Benchmark Publishers Limited.
Gobir, Y. A. (2002) “Iskoki a Idon ’Yan bori da Masu Ruƙiyya”. Kundin digiri na biyu. Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Gobir, Y. A. (2010). “Hulɗar Soyayya Tsakanin Ɗan’adam da Iska” a cikin           KONJOLLS: Kontagora Journal of Languages and Literatures. Kontagora: FCT.
Greenberg, J. (1946). The Influence of Islam Sudanese Religion. Monographs of the American Ethnological Society. New York Seattle. London.
Hamza, M. W. (1977) “Magungunan Hausawa”. Kundin digiri na farko, Jami’ar Bayero. Kano.
Ibrahim, S. M. (1982). “Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci            Kan Hausawa” Kundin digiri na biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Isma’ila, H. A. (1991). “Islamic Medicine and Its Influence on Traditional Hausa Practitioners in Northern Nigeria. Unpublished Ph.D Thesis. Madison: University of Wisconsin.
Imam, A. A. (1999) Ruwan Bagaja, Zaria: Nothern Nigeria Publishing Company.
Ingawa, A. (1969) Ruwan Bagaja. The Water of Cure. Fassarar Hausa zuwa Ingilishi. Zaria: Nothern Nigeria Publishing Company.
Kudan, M. B. T. (1987) “Kwatanta Jigon Ƙagaggun Labaran Gasa.” Kundin digiri na farko, Jami’ar Ahmadu Bello. Zariya
Malumfashi, I. (1996) “The Making of Abubakar Imam’s Ruwan Bagaja: A Preliminary Investigation.” Maƙalar da aka gabatar a taron ANA Arewa House, Kaduna.
Malumfashi, I. (2009) Adabin Abubakar Imam, Sokoto: Garkuwa Media Services Ltd.
Mora, A. A. (1989) Abubakar Imam Memoirs. Northern Nigerian Publishing Company. Zaria.
Mukhtar, I. (2004) Jagoran Nazarin Ƙagaggun Labarai, Kano: Benchmark Publishers Limited.
Tremearne, A. J.  N. (1913) Hausa Superstitions And Customs. Oxford: John Bale Sons and Danielsson,  Ltd.
Tukur, A. (1988) “Nazari a kan Cututtukan da suka shafi Fatar Jiki da Magungunansu a Bahaushiyar Al’ada.” Kudin digiri na farko, (B. A. Hausa) Jami’ar Bayero. Kano.
Yahaya, I. Y. (1988) Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. Zaria: Nothern Nigeria Publishing Company.
Yunusa, M. M. (1985) “Kasancewar Tatsuniyar Ruwan Bagaja tushen littafin Ruwan Bagaja na Abubakar Imam” Kundin digiri na farko, Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Sakkwato.




[1] Dubi Calvin Y. Garba (1990) “Kamus na Harshen Hausa” Evans Brothers (Nigeria Publishers Ltd) shafi na 75.
[2] Daga cikin sunayen iskoki na gargajiya akwai: Kayehi da Ɗantsatsumbe da Doguwa da Inna da Jitakuku da Gajimare da Kure da Duna da sauransu.
[3] Domin ƙoƙarin neman buwaya ga jama’a ake samun Sarakuna da Fatake da Tajirai da Mayaƙa da Ɓarayi da mutanen alfarma cikin jama’a, suna neman yin tsafe-tsafen baduhu da zana da kauda da fasa-taro da shashatau da sauransu.
[4] Tatsuniyar Gizo da sarki ita ce, inda Gizo ya je gonar sarki yana tsinke ɓaure yana sha har ya gama, ya koma wurin sarki ya ce ya gama aiki, ashe akwai wata tsuntsuwa tana saman wata itaciya tana kallon duk abin da Gizo yake yi. Bayan an kai masa amarya da gararta gida, sai ta fara rera waƙa cewar Gizo ya ci ɓaure ya sha ruwa ya sakace haƙoransa ya kurkure bakinsa, domin kar a gane cewa ya ci ɓaure. Bayan an saurari tsuntsuwar da kyau, sai aka mayar da amarya gida da gararta, shi kuma ya ji kunya ya rasa ta.

[5] Wannan ya yi kama da wani labari da ake bayarwa, wanda ya faru a garin Kaduna a Masallaci. Wani ladanin masallaci ne ya tsinci zobe a cikin masallacin, bayan an watse daga sallar Subahin. Da ya zo da zoben gidansa, da niyyar cigiyar wanda ke da zoben. Cikin rashin sani, ya shafi zoben, sai ya koma kan mutum, yana cewa, “zafi nake ji, zuba mun ruwa”. Yana zuba ruwan sai ga kuɗi ’yan naira dubu-dubu, suna fitowa daga bakin kan. Da Ladan ya dawo ya yi cigiyar zoben, ashe na wani hamshaƙin mai kuɗi ne, kuma sananne a cikin Kaduna.

No comments:

Post a Comment