Historians
as well as anthropologist affirm that the Hausas were living a life of mutual
co-existence and assisting of one another. They help one another on matters
concerning ceremonies, i.e. marriage and birth ceremonies, as well as
condolence i.e. for death and/or any situation of depression. However, the
cooperative practices amongst the Hausas include; eating together, teamwork and
settling scores between individuals among host of others. An interesting
phenomenon lies on the way younger ones are brought up with the orientation of
mutuality. The younger ones eat, play as well as listen to folklores together.
More so, any adult corrects whichever wrong they might do during these affairs.
This had made the orientation of younger ones an easy task for the Hausas
belief that, ‘the child….
Yakubu Aliyu
Gobir
Abstract
Historians as well as anthropologist affirm
that the Hausas were living a life of mutual co-existence and assisting of one
another. They help one another on matters concerning ceremonies, i.e. marriage
and birth ceremonies, as well as condolence i.e. for death and/or any situation
of depression. However, the cooperative practices amongst the Hausas include;
eating together, teamwork and settling scores between individuals among host of
others. An interesting phenomenon lies on the way younger ones are brought up
with the orientation of mutuality. The younger ones eat, play as well as listen
to folklores together. More so, any adult corrects whichever wrong they might
do during these affairs. This had made the orientation of younger ones an easy
task for the Hausas belief that, ‘the child belongs to everybody. These
cooperative activities have brought great development and understanding among
Hausas and their neighbors as well. This paper strives to showcase such
cultural practices, which promote mutual understanding among the Hausas. This
is a challenge to the individualistic life of the 21th century. Finally, the
paper presents some suggestions as panacea to the Hausas social life of today,
which is highly individualistic and self-centered. One of such is reviving such
cultural practices, which promotes mutual co-existence, though with
modifications so that they fit the modern world notwithstanding.
1.0
Gabatarwa
A goshin ƙarni na ashirin da ɗaya, al’adun Hausawa sun shaidi sauye-sauye da dama, a
ɓangarorin rayuwa daban-daban, da suka haɗa da zamantakewa da harkokin mulki da tattalin arziki da sauransu. Bisa
ga haka, ya zama dole idan za a kalli al’adun Hausawa a yau, a kalle su ta
fuskar zanguna uku, kamar haka: zangon na farko shi ne lokacin da suke Hausawa
tsuransu, wato cuɗanya da wasu ƙabilu da al’adu ba. Zango na biyu shi ne lokacin suka rungumi Musulunci.
Sannnan zango na uku shi ne lokacin da aka samu ƙarin tasirin zamananci a cikin al’adun. Wannan shi ya
jawo hankalin wannan muƙala na hango waɗansu al’adun Hausawa a zangon na na farko da kuma na
biyu, waɗanda suka ƙarfafa haɗin kai da samar da zaman lafiya tsakanin Hausawa a
wancan lokacin, domin ya zama darasi ga na baya, wato waɗanda suka samu kansu a zango na uku.
Kasancewar adabi, wani madubin da za a iya dubawa a
hango yadda kowace al’umma ke tafiyar da rayuwarta, ya sa wannan muƙalar duba wani sashe na adabin Hausawa, wato karin
magana, domin auna nauyin yadda Hausawa suke ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kai a tsakaninsu. Dubi waɗannan karin
maganganu da idon rahma:
Ø Kowane Tsuntsu kukan gidansu yake yi.
Ø Hannu Ɗaya ba ya ɗaukar jinka.
Ø Abotta a ƙafa take.
Ø Hannunka ko ya ruɓe ba ka yanke shi.
Ø Kar a mai da ƙurji gyambo.
Ø Zaman lafiya ya fi zama ɗan sarki
Ø Mai haƙuri yakan dafa dutse ya sha romo.
Ø Bin na gaba bin Allah.
Ø Ɗan’uwa rabin jiki.
2.0 Tsarin
Zamantakewar Hausawa
Tsarin zaman al’ummar Hausawa na yau da kullum tsari ne da
aka fara shi daga kan iyali. Daga iyali ne al’umma ko jama’a suke faruwa har su
zama babban gida, daga nan sai ’yar unguwa. Ire-iren waɗannan unguwanni ne suke haɗuwa su kafa ƙayyuka, ta haka ne kuma aka sami garuruwa da birane waɗanda sarakuna suke mulki.
A tsarin zaman Bahaushe, a gida guda ana iya samun magidanci ɗaya ko biyu ko ma fiye da haka waɗanda duka daga yannai sai ƙannai, ko dattijo da ɗiyansa. Dattijo yana da gona da ake kira gonar gandu,
inda kowane ɗa namiji zai ba da tasa gudunmuwa
wajen noman ta a kowace shekara. Idan kuma aka kawo amfanin gonar da aka noma
gida, a taru a yi amfani da shi ga dukkan iyali. A wasu iyalan, idan yaro ya yi
aure akan fitar da shi gandu, a ba shi tashi gona domin ya ɗauki ɗawainiyar kansa shi kaɗai. Irin wannan tsari, yana nuni da cewa ana zama ne a bisa tafarkin cuɗan-ni-in-cuɗe-ka da taimakon juna.
3.0 Al’adun Hausawa na Haɗin Kai da Taimakon Juna
Al’adun Hausawa masu samar da haɗin kai da taimakon juna suna da yawa, ta kowane ɓangare na rayuwa. Wasu daga cikinsu su ne:
3.1 Wasanni
Al’adun Hausawa sun samar da wasanni daban-daban a
matakin rayuwa daban-daban da ake gudanarwa. Akwai wasanni a matakin yarinta da
samartaka da kuma na manyanci. Akwai kuma na maza da na mata.
3.1.1 Wasannin Yarinta
Yarinta zangon shekaru ne da kan fara daga shekarar
haihuwa har zuwa kimanin shekara sha ɗaya ko sha
biyu. A matakin yarinta, sukan yi irin waɗannan wasanni ne a wuraren da yara suka taru don su yi hira a dandali ko
gidajen amare. Sun fi yin irin waɗannan wasanni da daddare, don lokacin yara ba su da
wani muhimmin aiki, amma kamar wasan gaɗa a wurin ’yanmata, ba lallai sai waɗannan wurare da aka ambata kawai sukan yi su ba, har ma sukan yi a wajen
bukukuwan aure da na suna da na salla, da dai sauransu.
Wasannin yara sukan tainmaka wajen inganta lafiyar
yara ta wajen motsa jiki da kawar da gajiya, suna kuma koyar da juriya da
jarunta. Haka kuma, kasancewar wasannin, a
ƙungiyance
ake yin su, suna ƙulla zumunta
a tsakanin yara, yadda yara za su zama abokai har zuwa lokacin girmansu. Sau da
yawa za ka ga dattijo yana raha idan ya haɗu da abokin wasansa, ko kuma mace in ta gamu da wadda suka yi wasa tare.
Shi ya sa sukan bi gida-gida suna kiran abokan wasansu. Daga cikin ire-iren waɗannan wasannin yarinta akwai:
• Wasannin Motsa Jiki. Misali: Darjin Dajina;
• Wasannin Tashe: misali: ‘Ka yi rawa Ɗanmalam’, ‘Tsoho da gemu’, ‘Zan buga, kar ka buga’ da
sauransu.
• Wasannin dandali:
Maza
– wasan sha iska, wasan ɓuya da sauransu.
’Yanmata
– wasan talle, wasan ɗankwali da sauransu.
• Sauraren
tatsuniya tare
3.1.2
Wasannin Matasa:
Matashi na farawa daga shekara ta goma sha uku har
zuwa shekara talatin da tara. Samari da ‘yanmata a wannan zango kan bayar da
gudunmuwa a cikin al’umma ta hanyoyi da dama, da suka shafi ayyukan gida da
gona da koyon sana’o’i musamman na gado. A bisa al’ada, akwai wasu ayyuka da
wasannin gargajiya da suke gudanarwa a ƙungiyance. Misalai, akwai wasan takkai da langa da
kalakuwa da kokowa da dambe da sauransu. Waɗannan wasannin sun taimaka musu wajen wartsake jiki da saka musu
karsashi da danƙon zumunci a
tsakaninsu.
3.1.3 Wasan
Barkwanci
Tukur (1994) yana da ra’ayin
cewa, ‘wasan barkwanci wasa ne da Hausawa ke gudanarwa ta hanyar zantuttuka a
tsakanin su, da suka haɗa da bayar
da ’yan gajerun labarai da suka taɓa faruwa ko
aka ƙirƙiro su da nufin daɗaɗawa ko tsokana don a yi dariya. Shi kuwa Sulaiman (2010) cewa
ya yi, ‘wasan barkwanci wata dangantaka ce da al’ada ta yarda da wanzuwar ta a
tsakanin al’ummu a duk inda suka haɗu sai sun
zolayi juna ko tunzura juna ba tare da samun wani saɓani ba’. Waɗannan
bayanai sun nuna cewa barkwanci na iya zama zantuttukan raha da ban dariya
tsakanin al’ummomi ko kuma yin ba’a tsakaninsu.
A ƙasar Hausawa, an lura cewa wasan barkwanci na taka muhimmiyar rawa wajen ɗinke ɓaraka ko
wata husuma a tsakanin jama’a, musamman idan aka lura da irin abubuwan da ke
faruwa tsakanin al’ummomin da ke wasa tsakaninsu. Misali, Gobirawa da
Katsinawa, ko Katsinawa da Haɗejawa ko
Kanawa da Zazzagawa da sauransu. Haka kuma, ko tsakanin masu sana’a ana samun
wasan barkwanci, misali, tsakanin ’yan gishiri da ’yan hamsin (masu sayar da
goro) ko tsakanin masunta da mahauta da sauransu. Bisa ga haka, ana cewa, ko
bayan nishaɗi, wasan
barkwanci yakan ƙarfafa danƙon zumunci tsakanin masu yin
sa. Alal misali, da wuya a ga Bagobiri ya yi fushi da Bafulatani ko Bakatsine.
Haka kuma, sanannen abu ne cewa wasan barkwanci yakan sauƙaƙe husumi tsakanin mace da ’yan uwan mijinta domin akan fashe
fushin juna a cikin wasa.
3.2 Aikin Gayya
Hausawa suna tafiyar da ayyukan
gayya don taimakon juna. Ana yin ayyukan gayya a gidaje inda ake yin sababbin ɗakuna da gyara tsofaffi da yin darnin gida ko na garka da ɗora ɗan bisan ɗaki da na rumbu da sauransu. Su kuma mata suna yin ayyukan
gayya don yin daɓen ɗaki da shafen jangargari da na farar ƙasa da sauransu. Ana kuma yin aikin gayya a gonaki inda ake yin sassabe da
huɗa da shuka da noma da girbi da ɗaurin amfanin gona da kawo shi gida. Haka kuma, cikin ƙayyuka da garuruwa ana yin ayyukan gayya wajen gyara masallatai da maƙabartu da magudanan ruwa da mashayar ruwa da gyaran hanyoyin da ake bi don
kawo amfanin gona gida.
3.3 Al’adun Karimci
Karimci, wata al’ada ce ta
girmamawa da taimakon juna a cikin al’umma. Hausawa suna al’adun karimci masu ɗimbin yawa a tsakaninsu. Daga cikin ire-iren al’adun karimci
akwai:
i.
|
Adashe
|
Ajiyar kuɗi ta karo-karo a bisa ƙayyadajjen lokacin da kowane mai yi zai ɗauka.
|
ii.
|
Ajo
|
taron bayar da gudunmuwa ga ango da nuna farin ciki
lokacin bikin aure.
|
iii.
|
Bashi
|
karbar wani abu musamman kuɗi da niyyar biya ko mayarwa bayan wani lokaci.
|
iv.
|
Buki
|
Kyauta ta gudunmuwa yawanci mata kan yi tsakaninsu
yayin da wata hidima ta same su.
|
v.
|
Ɗauke
|
wata al’ada ce ta bai wa wani rancen hatsi, sai ya
shiga da kansa da tsawonsa (igiya) daidai faɗin gabansa, ya ɗebo
hatsin, sai ya dawo da tsawon ga mai hatsin, sai kaka ta yi, sai ya zo ya
amshi tsawon ya je ya ɗauro dame kamar yadda ya ɗauro wancan lokaci, ya kawo wa mai hatsin, kuma ya
yi godiya.
|
vi.
|
Ɗaure
|
a bai wa mutum kiyon ramammiyar dabba, idan ta
haihu, na farkon na mai kiyo na biyu na mai ita.
|
vii.
|
Ɗegiya
|
bayeyeniyar abinci tsakanin maƙwabta.
|
viii.
|
Kaiwa
|
kyauta musamman ta alfarma zuwa ga
sarakuna ko manyan mutane.
|
ix.
|
Kari
|
mutum ya nuna bajinta a ba shi kuɗi, musamman wurin biki ko ga makaɗi.
|
x.
|
Kyauta
|
bai wa mutum wani abu don ra’ayi ba
tare da ya yi wani aiki ba.
|
xi.
|
Rance
|
amsar bashin kuɗi daga wani zuwa wani cikin gajeren lokaci.
|
xii.
|
Tugu
|
nau'in taimakon kasuwancin Bahaushe ne da yake yi wa
wani sanannen ɗan kasuwar da ya karye, sai ya je kasuwa ba ya da ko kwabo, a ba shi
kaya (haja) sai ya sayar ya cire tasa ribar.
|
xiii.
|
|
lada da akan ba wanda ya kai wata kyauta don nuna
yabawa da kyautar da aka yi.
|
Wasu
ke nan daga cikin ayyukan taimakekeniya da nuna karimci tsakanin Hausawa, kuma
waɗanda suka taimaka wajen ɗinke al’ummar Hausawa da samar da haɗin
kai tsakaninsu.
3.4 Matakin Manyanci
Akan saka rigar
manyanci ne daga
shekara arba’in zuwa abin da ya haura shekara sittin. Idan an cim ma wannan
matsayi an kai zangon shiriya ke nan, domin an yi aure, watakila har ‘ya’ya da
jikoki. Haka kuma, a wannan zango akan fahimci abubuwa da rarrabewa tsakanin
fari da baƙi ko
tsakanin gaskiya da ƙarya. Masu
wannan rukuni su ke jagoranci ga al’ammuran rayuwa. Kuma su ne jagaba wajen
sha’anin wasanni da bukukuwa da ayyukan gayya na sa kai ko taimakon kai da kai.
A bisa al’ada, Hausawan da ke cikin wannan rukuni
sukan yi wasu ayyuka tare da juna waɗanda ke ƙarfafa zumunci tsakaninsu. Misali: sukan ci abinci
tare, lokacin cin abincin dare, sai kowane magidanci ya zo da nashi abincin, a
harhaɗa shi wuri ɗaya a kewaye
ana ci tare, ana yi ana hira. Muhimmancin wannan al’ada shi ne taimaka ma mai ɗan ƙarfi, ko
wanda bai samu yin abincin a gidansa ba.
Haka
kuma, daga ayyukan waɗanda suka sanya
rigar manyanci shi ne sulhunta rigingimun da ke tasowa tsakanin matasa, ko ma
tsakanin su manyan, ko iyalansu, musamman da yake shugabannin al’umma mafi yawa
daga rukuni suke. Saboda haka, ƙoƙarin fito da hanyoyin zama
lafiya da ƙarfafa haɗin
kai shi ne aikin manya da shugabanni. Haka abin yake a wajen wasu ayyukan,
kamar kashin gobara
da zaman maokoki idan an yi rasuwa, da sauransu
3.5 Naɗewa
Zaman lafiya da samun haɗin kan jama’a a kowace al’umma shi ne ginshiƙin ci gabanta. Sai dai cuɗanyar Hausawa da wasu ƙabilu da al’ummomi musamman daga ƙetare (Turawa), ya haifar da rauni ko salwantar wasu
daga cikin waɗannan al’adun. Hausawa sun ce ‘Allah wadan naka ya
lalace’, wai in ji ɓauna da ta ga shanun noma’. A wannan zamani, ire-iren
waɗannan al’adu masu ƙarfafa haɗin kai sun
yi rauni saboda tasirin zamananci a cikin al’ummar Hausawa. A yanzu mafi
yawancin Hausawa suna zaune ne a bisa tafarkin ‘kowa tasa ta fisshe shi’.
Shawarwari
Bisa
ga abin da ya gabata na salwantar al’adun karimci da na taimakon kai da kai,
akwai bukatar manya da shugabanni da hukumomi su waiwayi waɗannan
al’adun, a shigo da su a cikin tsarin manhajar karatu, domin cusa tarbiyya da
ladabi da biyayya a zukatan matasa, domin su ne manyan gobe, ko da kuwa ta kama
ne a yi wa al’adun kwaskwarimar da za su dace da zamani.
Manazarta
Abdulƙadir, D
(2004), “Gyara Kayanka: Tasirin Al’adun Hausawa ga Cigaban Ƙasa.” A
cikin, Studies in Hausa Language, Literature and Culture, the Sixth Hausa
International Conference. Centre for the Study of Nigerian Languages: Kano.
Bayero University.
Abdullahi,
I.S.S. (2008),“Jiya ba Yau ba: Waiwaye a Kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawa
na Aure da Haihuwa da Mutuwa.” PhD
Thesis Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
Adamu, M. (1978), The
Hausa Factor in West African History. Zaria/Ibadan: ABU Press/Oxford University
Press of Nigeria.
Adamu, M. T. (1997), Asalin Hausawa da Harshensu.
Dan Sarkin Kura Publishers, Kano
Ibrahim, S.M. (1982),
“Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Hausawa.” Kundin Digiri Na Biyu Sashen Koyar da Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Sulaiman, U. (2010),
“Barkwanci a Ƙasar
Hausa”. Kundin digirin farko. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya: Sakkwato:
Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
Tukur, A. (1994), Wasannin
Barkwanci a Ƙasar
Hausa. Kano: Rukhsa Publication.
Umar, M.B. (2009), Wasannin
Tashe. Zaria: NNPC.
Yahaya, I. Y. (1977) Tatsuniyoyi
Da Wasanni:Littafi Na Biyar: Zaria: Oxford University Press.
Yahaya, I. Y. (1979) “Oral
Art and the Socialization Process: A Socio Folklories Perspective of Initiation
from Childhood to Adult Hausa Community Life”. Ph.D Thesis, Bayero University
Kano.
Yahaya, I. Y. (1982) Labarun
Gargajiya 2: Ibadan: University Press Limited.
No comments:
Post a Comment